Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, ta shawarci mata a kasar da su daina yin sa’insa ko fada da mazansu yayin da sabani ya gibta tsakaninsu a gida.
Ministar ta bayar da shawarar ne a yayin wani taron kwamishinonin ma’aikatun mata na jihohi a Najeriya, wanda aka yi a ranar Laraba a Abuja.
Kennedy-Ohaneye ta ce guje wa cacar baki zai hana cin zarafi da ka iya kai ga jin rauni ko mutuwa. “Ina kuma rokon mata akan kada su tsokano rigima, koda kuwa a gida ne. Ku zauna lafiya a gidanjenku saboda idan akwai zaman lafiya a gida, toh macen ciki ce ta bayar da gudunmawar kaso 80 cikin dari a ciki. “Idan kina bukatar zaman lafiya, toh za ki iya cimma hakan. Ki yi shiru da bakin ki.
“Mayar da martani ba zai haifar da ‘ya’ya masu idanu ba, maimakon haka zai kai ga mutuwa ko barna, yana haifar da tayar da yara marasa tarbiya cikin al’umma. “Ki yi shiru da bakinki, ba yana nufin baki da wayo bane illa dai ki zama mace mai hikima.
Idan namiji yana ihu tare da fadin maganganu, yi kamar mara wayo sannan ki yi shiru da bakinki.