Ministan tsaron ?asar nan, Bashir Magashi, ya ro?i kiristoci da su yi ma sojojin ?asar nan addu’a don kawo ?arshen ta’addanci.
A wani jawabi da ya fitar ran Asabar ta hannun mai taimaka ma ministan kan harkokin ya?a labarai, Mohammad Abdulkadri, Magashi ya ro?i mabiya addinin kirista da su yi amfani da wannan damar ta bikin ista su ro?i dawowar zaman lafiya a ?asar nan.
Ministan ya ce, lokacin biki ista lokaci ne da yakamata mu ro?i taimakon Ubangiji ya shigo lamurran mu don samun hanyoyin magance ?alubalen tsaro da muke fama da shi.
A kwanakin baya ne dai aka ruwaito Ministan tsaron na bayanin cewa tsaro ya samu a Najeriya, ya kuma bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Sanata Wamakko a ofishin shi dake birnin tarayya Abuja.