Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban lauyan gwamnatin Tarayya, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi gargadi mai zafi ga Alkalan Nijeriya akan su rika mutunta dokokin shari’a da kotu tare da gujewa mayar da shari’a wata haja da ake yin cinikinta ta yadda zai zama wanda ya fi kudi ne zai rika kwasar garabasar shari’a.
Dr Umar Jubrilu Gwandu, mataimaki na musamman kan harkokin ya?a labaran a ofishin babban lauyan shi ne ya fitar da wannan bayanin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa; Minista Malami ya yi wannan gargadin ne a taron shekarar shari’a ta 2021 da aka gudanar a kotun daukaka kara da ke Abuja.
Malami ya ja hankalin Alkalai kan tabbatar da adalci da kare martabar aikinsu wajen aiwatar da hukunci da kuma bai wa al’ummar kwarin gwiwar aminta da ?angaren shari’a.