Mijina Ba Raggon Namiji Ba Ne – Uwargidan El Rufa’i

Hajiya Hadiza El’rufa’i ta wallafa wani rubutu cikin raha da barkwanci a shafinta na Twitter tana mai cewa duk da kai kawona a cikin dakin “Za OZA Room” domin ganin Mace ta haye Karagar Sarautar Zazzau, El’rufa’i ya zabi namiji a sarautar Zazzau!.

Yanzu duk Duniya kowa yasan bani da tasiri akan mijina, shi ba mijin Hajiya bane shi ba mijin tace bane, ba raggon Maza ba ne..

Masu karatu idan baku manta ba uwargidan Gwamnan dai kwanaki ta nuna ra’ayinta kan a maye gurbin Sarautar Zazzau da Mace, lamarin da ya haifar da surutai a faɗin Najeriya, inda wasu ke ganin kalaman matar gwamnan kamar rashin martaba Sarauta ne.

Daga baya dai Uwargidan Gwamnan ta sake wani rubutu a shafinta na tiwita inda ta bayyana waccan maganar ta ta a matsayin raha.

Gwamna El Rufa’i dai ya kasance wani Gwamna mai son wasa da barkwanci da iyalansa, kuma ya zama Gwamna ɗaya tilo a Najeriya da ke da Matan aure har guda Uku.

Labarai Makamanta