Messi Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallo Na Duniya


Dan kwallon tawagar Argentina mai taka leda a Paris St Germain, Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana, karo na bakwai kenan a tarihi.

Bayan da ya bar Barcelona kan fara kakar bana, Lionel Messi ya kara lashe babbar kyautar tamaula a duniya ta kashin kansa, duk da Barcelona na fuskantar kalubale a kakar nan.

Messi wanda ya karya tarihin yawan kwallon da Pele ya ci a kungiya daya – dan kasar Argentina ya ci kwallo a kalla 20 a kaka 13 a jere a Turai, shine kan gaba a bajintar a manyan gasar Turai biyar.

Haka kuma ya doke tarihin Gerd Muller na cin kwallo 30 a kaka 12 a kungiya daya da haura tarihin da Xavi ya yi na kan gaba a yawan buga wa Barcelona tamaula.

Haka kuma Messi ya dauki Copa America da Argentina, kofin da ya dade yana mafarki a tarihi – wanda kofin duniya ne ya rage masa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply