?ungiyar mata ?an majalisa ta tarayya ta yi kiran a na?a mace a matsayin ministar tsaron ?asar domin shawo kan matsalar tsaro.
Shugabar kwamitin majalisar wakilai kan mata Taiwo Oluga ce ta yi kiran ranar Litinin a lokacin taron ganawa da manema labaru a Abuja.
Ta ce Idan har aka na?a mace a matsayin ministar tsaro, to kuwa za a ga aiki da cikawa, za ku ga sauyin da za a samu a ?angaren tsaro.
Ta nuna takaici kan yadda Najeriya ta kasance a baya-baya wajen shigar da mata a harkar gwamnati.
Ta ce bayanai na nuna cewa koda dukkanin matan da za su tsaya takara a Najeriya za su yi nasara, za a ci gaba da fuskantar matsalar ?arancin mata a tafiyar da lamurran gwamnati.