Maza Sun Gaza Lokacin Ba Mace Ministan Tsaro Ya Yi – Kungiyar Mata

Ƙungiyar mata ƴan majalisa ta tarayya ta yi kiran a naɗa mace a matsayin ministar tsaron ƙasar domin shawo kan matsalar tsaro.

Shugabar kwamitin majalisar wakilai kan mata Taiwo Oluga ce ta yi kiran ranar Litinin a lokacin taron ganawa da manema labaru a Abuja.

Ta ce “Idan har aka naɗa mace a matsayin ministar tsaro, to kuwa za a ga aiki da cikawa, za ku ga sauyin da za a samu a ɓangaren tsaro.”

Ta nuna takaici kan yadda Najeriya ta kasance a baya-baya wajen shigar da mata a harkar gwamnati.

Ta ce bayanai na nuna cewa koda dukkanin matan da za su tsaya takara a Najeriya za su yi nasara, za a ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin mata a tafiyar da lamurran gwamnati.

Labarai Makamanta

Leave a Reply