Shahararen mawakin Afrobeats Davido ya ce zai ba gidajen marayu da ke Najeriya zunzurutun kudi har naira miliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka dubu dari 608, bayan da magoya bayansa suka aika masa da kudi.
A baya baya nan ne mawakin ya nemi magoya bayansa da suka yi intifakin cewa ” ya yi mu su wakar da ta kasance bakandamiyya ” da su tura masa da kudi zuwa wani asusun ajiyar kudi da ke dauke da sunansa.
A ranar Asabar ce Davido ya ce ya gabatar da kokon barar ne “cikin raha” , amma yawan wadanda suka amsa kiran nasa ya zarce yadda ya rika tsammani.
Ya godewa wadanda suka ba da gudunmmawar kudi, yayin da ya bayyana yadda za a yi amfani da su.
Kason da za a raba wa gidajen marayu ya hada da wanda magoya bayansa suka aike masa da kuma gudunmmawar naira miliyan hamsin da wani ya bayar.
Ana yi wa Davido kallon daya daga cikin manyan shahararun mawakan Afrika.
Ya ci lambar yabo ta MTV da BET kuma ya yi aiki tare da wasu shahararun mawakan kasashen waje da suka hada da Chris Brown da Nicki Minaj.
Bukatar da ya gabatar ata kafofin sada zumunta ta janyo ra’ayoyi mabanbanta daga masu bibiyarsa.
Wasu sun ce mawakin mai magoya baya miliyan 22 a shafin Instagram a wasu lokutan ya na son ya nuna yadda yake rayuwar kasaita a shafin intanet.
A wani sakon da ya wallafa a shafin Twitter, Davido ya ce manufarsa ita ce ya tara kudi domin ya samu damar shigo da motarsa ta Rolls-Royce daga tashar jirgin ruwa.
Sannan ya tura da bayanan asusun ajiyar kudi na banki tare da rarraba hotuna yayin da adadin kudin da ke ciki ya ci gaba da karuwa a ‘yan kwanaki.
A sanarwar da ya fitar ranar Asabar mawakin ya ce manufarsa ita ce ya ga tara wannan kudi a zagayowar ranar haihuwarsa a kowace shekara domin taimakawa alumma.
“Ni mai son taimakawa mutane ne ,” in ji shi.