Shugaban Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya yi kira ga al’ummar Musulmi da yin koyi da halayen Manzon Allah, a daidai lokacin da ake cigaba da gudanar da bikin Maulidi.
Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin sakon murnar bikin Maulidi da ya fitar, inda ya bukaci jama’ar musulmi da rungumar halayen Manzon Allah na so da taimakon juna da nuna jin kai a tsakanin al’umma.
Ramalan ya ƙara da cewar hakika haihuwar Manzon Allah ya kasance alheri da nasara wadda ta game dukkanin mutane sakamakon yadda haihuwar ta kawo haske da rahama a duniya gaba ɗaya.
Tijjani Ramalan ya shawarci dukkanin jama’a da suyi amfani da wannan lokaci na bikin Maulidi wajen sanya Najeriya cikin addu’a na Allah ya fitar da kasar daga manyan matsalolin da ta tsinci kanta a cikin na tsaro da tsadar rayuwa.