Yayin da Nijeriya ke bikin haihuwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba 2020, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Nijeriya kan wasu muhimman batutuwa guda biyar.
- Ku Nuna Kauna Da Fahimta Ga Sauran ‘Yan Uwanku ‘Yan Kasa: Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Naieriya da su yi amfani da wannan biki wajen koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar nuna kauna da fahimta ga al’umman kasar. Ya kuma bukaci su bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa
- Sako Ga Matasan Nijeriya: Da yake misali da yawan rikice-rikice da sace-sace da aka fuskanta a fadin kasar bayan wasu bata gari sun janye zanga-zangar EndSARS, Shugaba Buhari ya bukaci matasan Nijeriya da su yi watsi da duk wasu munanan halayya.
- Za A Hkunta Wadanda Suka Yi Sace-sace: Shugaba Buhari ya sha alwashin tabbatar da hukunta dukkanin wadanda ke da hannu a sace-sacen kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kansu a fadin kasar.
- Hukunta Azzaluman Jami’an ‘Yan Sanda: Buhari ya kuma tabbatar da cika alkawarinsa na yin adalci ga duk wanda jami’in ‘yan sanda suka zalinta.
- Gargadi Akan Annobar Corona: Shugaba Buhari ya bayyana cewa zuwa yanzu Nijeriya ta yi nasarar magance matsalar ta hanyar tabbatar da adadin mutanen ya yi kasa.
Ya kuma shawarci duk ‘yan Nijeriya da su kiyaye dokokin kamuwa daga cutar COVID-19, kamar wanke hannaye, saka takunkumi da dokar nesa-nesa da juna.