Abubakar Muhammad Genaral yana cikin ‘yan kwamiti na jihar Kano na daukar maaikata da gwamnatin tarayya ta nada amma wasu yan kwamitin suke kokarin cire shi a cikin kwamitin ga abinda ya bayyana a shafinsa na Facebook:
Labari ya zo min cewa ana ta cece kuce a kafafan yada labarai akan cireni da akayi daga kwamatin Samar da aikin yi 774,000 na gwamnatin tarayya da shugaban kasa ya nada kuma Allah ya kaddara ni acikin mutum 20 da aka turo jihar Kano.
-Gaskiya ne cewa wasu sun kalubalanci kasancewa ta a cikin wannan kwamati daga Kano.
-Gaskiya ne cewa maaikatar Matasa da wasanni ta jihar Kano sun tura wasika Abuja zuwa offishin ministan kwadago da samar da aikinyi inda takardar ke gabatar da wanda ya maye gurbi na.
-Gaskiya ne cewa wata wasikar mai Kama da sa hannun ministan kwadago da samar da aikinyi na yawo a yanar gizo cewa ya dakatar da ni daga kasancewa mamba a wannan kwamiti, duk da cewa baa fadi wani dalili na dakatar da ni din ba.
Matsaya ta: Tun faruwar wannan alamari ga abinda nace a cikin what’s up group na duk mambobin wannan kwamiti na mutum 20:
“INNA LILLHI WA INNA ILAIHI RAJIUN. INNA LILLHI WA INNA ILAIHI RAJIUN. INNA LILLHI WA INNA ILAIHI RAJIUN.
ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WAAKHLiGNI KHIRIN MINHA.
ALLAHUMMA MAN ARADNA BIDURRIN, FARUDDA KAIDUHUM FI NAHARIHI.
LAHAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, ALALIYU, ALAZEEM.
I stand for the Truth and I refused to be intimidated.
Tun daga wannan lokaci ake tuntuba ta akan wannan batun, har da yan jaridu, dan kawar da shakku akan rade radin da suke ji a gari, amma ni ina kokarin baiyyana iya abin da na fada a baya.
Kwatsam sai naji hira da akayi da mataimakin shugaban wannan kwamiti na jihar Kano a gidan rediyan freedom inda yake ambatan suna da mukamin maigirma kwamishinan maaikatar Matasa da wasanni Hon. Kabiru Ado Lakwaya inda ya ce shine ya neme su da bukatar a canja sunana da wani. A ta cewarsa, sun yi kokarin fahimtar da kwamishinan akan alamarin amma ya rubuta wasika Abuja.
Amma mai girma kwamishina ya kirani akan wannan alamari kuma ya tabbatar min da cewa ba haka bane, kuma bashi acikin wannan zagon kasan.
SHAWARA TA:
Ina shawartar masu maganganu akan wannan batu, musamman ma a kafofin yada labarai da su daina yamutsa hazo.
Ni dai na FAUWALA WA ALLAH komai. Kuma ni a fahimtata, wadanda ke da hannu akan wannan alamari suna kokarin yi wa Allah gyara ne (waiyazubillah) shi kuma Allah yana madakata.
Allah, Shine masanin abinda yake boye ko abinda aka baiyyana. Ina rokon Allah da ya yi min zabi mafi Alheri. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
- A bisa tarbiyar da na samu wajen iyaye, malamai da sauran magabata. Idan aka fauwala wa Allah komai, to ba a so kuma a dinga yamadidi akai. Akan haka nake shawartar musamman masoya da cewa, kar a biyewa wayanda suke kirkirar maganganu dan su farantawa iyayen gidan su. Lauyoyi da jamian tsaro zasu yi aikin su akan kowanne furuci da yardan Allah.
Ina godiya ga alumarmu da suka taya mu alhini da adduoi, wadanda ban sansu ido da ido ba, amma sun jajirce akan Allah ya yi mana zabi mafi alheri. Ya kuma shiryi masu yi mana Zagwan kasa.
Na gode. Allah ya sa mu gama da wannan fili na duniya lafiya.