” ‘Yan ta’addan yankin Naija-Delta da suka addabi Najeriya a shekarun baya da ta’addanci da fashe fashen bututun mai suna yin haka ne bisa ga manufar da suke da ita a yankin su na cewar ayyukan hakar mai na ɓata gonaki da muhallin su saɓanin ‘yan bindigar yankin arewa maso yamma dake ta’addanci babu dalili, wannan shine babban banbancin dake tsakanin ‘yan bindiga da’yan Neja Delta”.
Kalaman tsohon Kwamishinan Shari’a na jihar Zamfara kenan Baraden Gumi Alhaji Muhammad Sani Takori a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da wakilinmu a Kaduna.
Takori ya kara da cewar sakamakon manufa da ‘yan Neja Delta ke da ita shi ya ba Gwamnatin Tarayya a wancan lokacin karkashin marigayi Shugaban Ƙasa Umaru ‘Yar’adua saukin samun zama dasu har aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya, wanda a ɓangaren ‘yan bindiga babu wata manufa da suke da ita wadda za a iya zama dasu, saboda haka masu ganin matsalar ‘yan bindiga iri guda ce da ta ‘yan Neja Delta sun yi kuskure.
Sani Takori wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne da ya wakilci kananan Hukumomin Gumi da Bukkuyum a majalisar ƙasa ya yaba matakan da gwamnatin Zamfara ke ɗauka a yaƙi da ‘yan ta’adda sai dai ya bayyana cewa aiki ne da ba gwamnati kadai ya kamata a zuba wa ido ba kowa na da irin rawar da ya kamata ya taka wajen cimma nasara.
Dangane da tataburzar da ta faru na neman shugabancin majalisar Dattawa kuwa Honorabul Sani Takori ya ce ya zama dole a yaba wa tsohon Gwamnan Zamfara Sanata Abdulaziz Yari bisa jajircewar da ya gwada wajen ganin shugabancin majalisar ya dawo shiyyar arewa maso yamma, ya nuna shi cikakken ɗan siyasa ne mai kishin ƙasa da yankin da ya fito.