Matsalar Tsaro: Zulum Ya Buƙaci Jama’ar Borno Da Ɗaukar Azumi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Asabar ya gana da malaman addinin Isalam da Kirista inda ya zabi Litinin matsayin ranar addu’a da azumi na biyu a fadin jihar.

Za’a yi addu’an ne domin neman zaman lafiya a jihar. Zulum a jawabin da yayi, yace ba don alfahari ko neman suna yake zuwa wurare masu hadari ba, amma kawai yana yi domin cika alkawarin da ya yiwa al’ummarsa.

“Ya ku al’ummar jihar Borno, bayan tattaunawar da mukayi yau, na alanta ranar Litinin, 19 ga Oktoba 2020 matsayin rana ta biyu da azumi a fadin jihar da addu’a na neman zaman lafiya a Borno.”
“Ina son bayyana cewa babu hutu ranar Litinin kuma babu wani taron addu’a. Kawai abinda ake bukata shine kyakkyawan niyya da komawa ga Allah yayinda muke azumi daga gidajenmu, ofishohinmu, kasuwanninmu, da wuraren ayyukanmu.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply