Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’an Tsaro A Zamfara

Rahotanni daban-daban sun tabbatar da mahara sun kashe mutum 42 a farmaki daban-daban a yankunan Zamfara da Katsina.

A Jihar Zamfara dai jaridar Daily Trust da wasu jaridu sun wallafa yadda aka bindige mutum 12 a ranar Alhamis a ƙauyen Magarya, cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi.

Daga cikin mutanen da aka kashe, har da jami’in tsaro na Askarawan Zamfara da mutum huɗu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Mohammad Shehu, ya tabbatar wa Daily Trust kisan ‘yan sandan mobal ɗin a Zamfara.

Kwamishinan ya ce maharan kimanin su 300 sun mamaye ƙauyen a kan babura.

“Sun kewaye jami’an tsaron mu suka buɗe masu wuta, nan take suka kashe ‘yan sanda bakwai, wasu da dama suka ji raunuka.

“Maharan ba su jin daɗin yadda ‘yan sanda ke hana su yin ta’addancin su tsawon shekaru.

“Tun da aka jibge ‘yan sanda a yankin, ‘yan bindiga sun kasa kai hare-hare a yankin,” cewar Dalijan.

Amma ya ce za a ƙara girke jami’an ‘yan sanda a yankin.

Wani mazaunin yankin ya ce wajen ƙarfe 5:10 na asubahi maharan suka kewaye ƙauyen, lokacin da ake shirin yin Sallah.

Ya ce ‘yan bindiga sun ƙone gidaje biyu da rumbuna da yawa, kuma sun saci raƙuma uku, shanu, tumaki da awaki. Amma ba su arce da mutum ko ɗaya ba.

“Lokacin da mahara suka dira, mutanen ƙauyen sun gudu cikin daji. Daga baya sun dawo an yi ƙidayar gawarwaki 12, cikin su kuwa har da ta ‘yan sandan mobal bakwai.

“Kuma wannan ne karo na huɗu zuwan su ƙauyen.

Labarai Makamanta

Leave a Reply