Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta baci akan rashin tsaro da kasar ke ciki bayan ‘yan fashi sun sace dalibai da yawa a Katsina.
A wata sanarwa Mista Atiku ya ce dole ne gwamnati ta yi watsi da tsofaffin dabaru ta rungumi dabaru masu kyau.
“Satar dalibai da yawa a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara a Jihar Katsina, wani lamari ne da ba a maraba da shi game da yawan rashin tsaro a cikin kasar, wanda na yi Allah wadai da kakkausar murya,” in ji Mista Atiku.
Atiku yace “Ina tausaya wa iyayen yaran da aka sace da gwamnati da mutanen Katsina.”
Shugaban kasa Buhari dai na cigaba da fuskantar matsin lamba da suka a ciki da wajen Najeriya dangane da halin da tsaro ya tsinci kanshi a ciki, biyo bayan kisan Manoma da ‘yan Boko Haram suka yi ta hanyar yi musu yankan rago a Jihar Borno, da kuma satar ?aruruwan dalibai da ‘yan Bindiga suka yi a lokaci guda a jihar Katsina, abin da ba’a taba samu ba a tarihin Jihar.