Matsalar Tsaro: Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi Ne Mafita – Uba Sani

IMG 20240310 WA0186

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan dalilan da yasa jihar ta kasa magance matsalar hare-haren ƴan bindiga. Gwamnan ya yi nuni da cewa an kasa shawo kan matsalar ne saboda ƴan sa-kai ba su da ingantattun makamai.

“Ƴan sa-kai ba za su iya riƙe abin da ya wuce ƴan ƙananan bindigu ba, amma waɗannan ƴan bindigan suna zuwa ne ɗauke da AK-47 da mugayen makamai. Wannan shi ne halin da muka tsinci kan mu a ciki.”

Gwamnan ya sake yin kira kan muhimmancin samar da ƴan sandan jihohi domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, Uba ya yi nuni da cewa samar da ƴan sandan jihohin zai ba mutanen ƙauyuka, damar riƙe makaman da za su kare kansu da su.

“Wannnan shi ne dalilin da ya sa wasu daga cikinmu suka dage cewa muna bukatar a samar da ƴan sandan jihohi. “Idan aka samar da ƴan sandan jihohi, za a ba su dama bisa dokar kundin tsarin mulki su riƙe makamai ciki har da AK-47.

Labarai Makamanta

Leave a Reply