Ambasada Salisu Bala Sulaiman wani mai fashin ba?in al’amurra ya bayyana cewa muddin ana son a samu kawar da matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya sai Gwamnonin Arewa sun kawar da banbancin siyasa a gefe daya, sunzo sunyi abinda ya dace karin a samu natija.
Ambasada Salisu Bala ya bayyana hakan ne a shirin DIALOGUE da ake gabatarwa na gidan Talabijin da Rediyo na liberty TV Abuja.
Idan ka duba yadda Gwamnanonin Katsina da Zamfara suka hada kansu duk da banbancin siyasar dasu ke dashi musamman kan matsalar garkuwa da daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnati dake kankara.
Kuma babu gwamnan da zai gaya maka baisan mafakar yan ta’addan jihar sa ba, indai har ansan inda mutanen nan suke me zai hana ayi anfani da dubaru na sirri a samo bayanan su akawo karshen su?
Inda ace sauran gwamnonin yankin arewa zasu tashi tsaye, su kauda banbancin siyasa suzo su duba matsalolin dake fuskantar yankin. Dole sai anyi anfani da sarakunan gargajiya wurin tattaro bayanan sirrin da zai tallafawa jami’an tsaron mu wurin kawo karshen matsalar tsaro.
Makudan kudaden da ake kashewa a fannin tsaro ba a kashe su yanda ya dace, domin sai an samu bayanan sirri kamin a iya samun nasarar kawo karshen matsalar tsaro wanda kuma gwamnatocin mu na arewa basa baiwa fannin muhimmancin da ya dace. Dole sai gwamnonin mu sun hada kai tare da sarakunan mu za a samu nasarar kawo karshen matsalar tsaro” kamar yanda Ambasado Bala Salisu Bala ya bayyana”