Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta nemi ta zauna da shugaba Muhammadu Buhari a madadin sanatoci 109 saboda halin da tsaro yake ciki a ?asar.
Ta ce bu?aci manyan hafsoshin tsaron kasar su gaggauta tura sojoji domin kare iyakokin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Majalisar ta yanke wannan shawarar ce bayan zamanta na yau Talata wanda a ciki ?an majalisar suka bayyana damuwa game da halin da tsaro yake ciki a kasar.
A cewar majalisar, akwai bukatar a hanzarta kafa sansanin soja da na yan sanda na din-din-din a kusa da kananan hukumomin Shiroro da Rafi da ke jihar Neja.
Kafin majalisar ta ?auki wannan matakin, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya ce la’akari da ?aruwar hare-hare a sassan ?asar, akwai bu?atar a yi ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari domin kawo maslaha mai ?orewa game da lamarin da ya zama abin kunya.
Ya bayyana haka bayan da abokin aikinsa Sanata Sani Musa ya yi nuni da dokar majalisar ta 42 da 52 da ta nemi majalisar ta gabatar da ?udiri kan ayyukan ?an bindiga da mayakan Boko Haram a kananan hukumomin Shiroro da Rafi da ke jihar Neja – lamarin da ya dauki wani salo na daban.
Sai dai a cewar Sanata Adetunmbi, matsalar tsaron ba wai Neja ta shafa ba, abu ne da ya shafi ?asar baki ?aya.
A ganinsa, abin da ke faruwa a Najeriya lamari ne da ka iya juyewa zuwa ya?i saboda a cewarsa, “cikin shekara 10 da ta gabata, akwai rahotanni da dama da suka nuna cewa Najeriya na iya shiga halin da take ciki a yanzu”.
Shi kuwa Sanata Ajibola Basiru da ke wakiltar Osun ta tsakiya cewa ya yi rundunar yan sandan kasar ta gaza tabbatar da tsaro a kasar a don haka yake ganin akwai bu?atar a bijiro da tsare-tsaren da za su magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya ce akwai bu?atar a ?ibi jami’an tsaro kimanin dubu biyar a kowace jiha.