Matsalar Tsaro: Majalisa Ta Nemi Buhari Ya Kori Shugabannin Tsaro

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya saboda gazawar da suka nuna.

Majalisar ta yi kiranta ne bayan bukatar hakan da Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Kashim Shettima ya gabatar a lokacin zamanta na ranar Talata.

Sanatocin sun sha aikewa da makamanciyar bukatar ta maye gurbin hafsoshin tsaron da sabbin jini masu fikirar dakile ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya, sai dai bukatar ta su ba ta samu karbuwa ba.

An shafe shekaru bangarori da dama na Najeriya na kira ga Buhari ya sallami Hafsohon Tsaron bisa zarginsu da gazawa amma ya bai amsa kiran ba.

A baya ya taba yi wa hafsoshin taron magana da kakkausar murya cewa ba su da uzuri kan ci gaban matsalar tsaro a Najeriya, har aka yi zaton damar karshe ce ya ba su kafin ya kore su.

A wancan lokacin, Buhari ya umarce su da su hada kai da Ministan Sadarwa domin dakile matsalar ta’addanci bayan da suka yi zargin cewa layukan waya marasa rajista da ‘yan ta’adda ke amfani da su na taimaka wa ta’addanci.

Kawo yanzu dai matsalar tsaro na karuwa a sassan Najeriya, kama daga ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, Boko Haram da barayin shanu da ‘yan fashin teku da sauransu.

Tabarbarewar tsaro a baya-bayan nan ta kara taso da kiraye-kirayen naman Buhari ya kori Hafsoshin Tsaron da ake zarin sun ma haura lokacin ritayarsu, baya ga su nuna gazawa a aikinsu.

Hafsoshin Tsaron da ake korafi a kansu su ne:

Babban Hafsan Rundunar Tsaro ta Kasa, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin
Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai
Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar
Da Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas
Tuni da Sanatocin suka amince da bukatar sauya hafsoshin da kuma aike wa Shugaban Kasa bukatar, sakamakon jan hankalin zauren Majalisar da Sanata Kashim Shettima ya yi kan abun da ya faru na kisan manoma 43 a Zabarmari, Jihar Borno.

Related posts

Leave a Comment