Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sake nanata kiransa ga gwamnatin tarayyar kasar cewa ta dauko sojojin haya daga kasashen wajen domin su taimaka mata murkushe kungiyoyin ‘yan tayar da kayar baya.
Gwamna Zullum ya fadin hakan ne a dazu a fadar Shugaban kasar da ke Abuja yayin wani taron manema labarai kan irin ci gaban da ake samu wajen yaki da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a jiharsa.
Ko a bara ma dai gwamnan ya yi irin wannan kiran, amma gwamnatin kasar ta kawar da yiwuwar bin wannan shawarar.
To bayan kammala taron; Gwamnan ya yi wa abokin aikinmu Haruna Shehu Tangaza karin bayani kan dalilansa na yin wannan kiran; amma ya fara ne da yi masa bayanin kan irin halin da ake cikin a yaki da kungiyoyin yanzu a jiharsa.