Matsalar Tsaro: Lissafi Ya Kwace Wa Tinubu – Amnesty

IMG 20240226 WA0252

Kungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ƴan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai ɗari biyu da tamanin da bakwai da malamai a yankin Kuriga a jihar Kaduna na nuna gazawar hukumomin Najeriya na kare al’umma daga hare-haren ƴan bindiga da suka kashe dubban ƴan ƙasar cikin shekara biyar da ta gabata.

Ƙungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da mutanen da aka sace domin haɗa su da iyalansu.

A cewar ƙungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na Najeriya tare da gabatar da sakamakon binciken ga al’umma sannan su tabbatar an hukunta waɗanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.

Amnesty ta ce, “sace-sacen mutane da dama a baya-bayan nan ƙarara sun nuna cewa shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su da tsayayyen tsari na kawo ƙarshen miyagun laifukan ƴan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan jihohin Najeriya. Duk matakan tsaron da shugaba Tinubu da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba sa tasiri,” in ji Isa Sanusi.

“Ganin yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a Najeriya a yanzu, a bayyane take cewa batun kare rayuwa da dukiyoyin al’umma ya na ƙasa cikin jerin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Bai kamata a ƙyale mutane su zauna cikin fargaba da tsoron hari da garkuwa ba.

Yawan gazawar hukumomin Najeriya wajen kare mutane abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ƙarshen sa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da waɗanda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama’a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar ɗaruruwan mutane cikin haɗari.

A ranar Alhamis ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna inda suka sace ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, sai dai malamin ya samu kuɓuta sai kuma ɗalibi guda da ya mutu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply