Matsalar Tsaro: Kowa Ya Kare Kanshi A Katsina – Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya umurci mazauna garuruwa a jihar Katsina da su tashi su kare kansu daga yawan hare-haren yan bindiga da masu satar mutane a jihar.

Gwamnan ya sheda hakan ne a wajen kaddamar da bude ofishin injiniyoyi na COREN reshen jihar Katsina a ranar Litinin kamar yadda Katsina Post ta rawaito mana.

Gwamnan ya bayyana cewa dole sai mutanen gari sun jajirce wajen bai wa garuruwansu tsaro ba tare da tsoro ba, ta hakan ne za a yi nasarar kawar da duk wasu yan ta’ada a fadin jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply