Matsalar Tsaro: Ina Zargin Buhari Ya Samu Ta?in Hankali – Ezikwesili

Tsohuwar Ministar ilmi, Madam Oby Ezekwesili ta nuna shakkunta game da lafiyar ?wa?walwa ta shugaban ?asa Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun ce Madam Oby Ezekwesili ta bukaci ayi wa lafiyar kwakwalwa da jikin shugaban kasa Muhammadu Buhari binciken kwa-kwaf.

Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar ta bukaci ayi wannan ne domin al’ummar Najeriya su san ko shugaban kasar na su ya na da koshin lafiya.

A cewar Oby Ezekwesili, halin da ake ciki yanzu a Najeriya na rashin tsaro, ya ci ace an tashi an san lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Ina tunani a wannan lokaci da kuma mummunan halin rashin tsaro da kasar nan take ciki, dole a hakura da maganar sirri, mutanen kasa suna da hakkin sanin halin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

“Dole mu duba lafiyar jiki da kwakwalwar shugaban kasar domin sanin ko ya na da ikon cigaba da sauke nauyin da ke kansa na gudanar da aikin ofishin shugaban kasa.” Inji Oby Ezekwesili.

“Mutanen kasa za su iya tursasa wa a kafa kwamiti mai zaman kansa, da zai taimaka mana da yi wa shugaban kasar gwaji domin sanin halin lafiyar da yake ciki.”

Ezikwesili ta ce kwamiti na dabam ya kamata ya yi wannan aiki, ba likitocin fadar shugaban kasa ba, ta ce ba za a yarda da ma’aikatan gwamnati ba.

Related posts

Leave a Comment