Gwamnonin Najeriya 36 sun yanke shawaran ganawa da shugaba Muhammadu Buhari nan ba da dadewa ba domin tattauna lamarin tsaro a fadin tarayya, musamman bisa abin da ya faru a Borno.
Gwamnonin sun yanke hakan a zaman da kungiyar gwamnonin Najeriya NGF a ranar Laraba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.
Gwamnonin da kungiyar ta aike jihar Borno domin jajantawa gwamna Babagana Umara Zulum ranar 1 ga Disamba sun dawo musu da bayanan abinda suka ganewa idanuwansu a Garin Zabarmari a karamar hukumar Jere ta jihar.
A takardar da kungiyar gwamnonin NGF ta fitar a Abuja ranar Juma’a, sun ce zasu goyi bayan duk wani abu da za’ayi domin gyara hukumar yan sanda.
Sha’anin tsaro dai na cigaba da fuskantar matsaloli a Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke addaba yankin Arewa maso gabas, yayin da Fulani ‘yan bindiga ke kisan mutane a yankin Arewa maso yammacin ƙasar da Arewa ta tsakiya.
Shugaban ƙasa Buhari na fuskantar matsin lamba a ciki da wajen ƙasar, inda wasu ke kiran shugaban da ya yi murabus bisa ga abin da suke gani na gazawa daga shugabancin sa.