Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Ayyana Dokar Ta Baci A Kananan Hukumomi 3

Rahoton dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle, ya ayyana dokar ta baci a kananan hukumomi uku da wasu garuruwa na jihar, bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga.


Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Anka, da Bukkuyum, da kuma Gummi.

Gwamna Matawalle ya kuma bayar da umarnin dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar nan take, ciki har da taron jam’iyyar APC sai baba ta gani, a wani bangare na matakan saukaka kokarin jami’an tsaro na fatattakar masu aikata laifuka a wadannan yankuna.

A sanarwar da ya fitar yau jumma’a, kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara ya ce an kafa dokar hana zirga zirgar ne don dakile yawaitar hare-hare a garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.

Ya bayyana cewa, daga yanzu an hana duk wata zirga zirga a wadannan kananan hukumomi da garuruwa da aka ambata.

Sanarwa ta kuma kara da cewa gwamnati na duba yuwuwar rufe kasuwanni a Danjibga da Bagega, haka kuma ta ce ta rufe wadannan hanyoyi da suka hada da Colony zuwa Lambar Boko, Bakura zuwa Lambar Damri, Mayanchi – Daki Takwas zuwa Gummi, Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri-Bawanganga-Wanke, Magami zuwa Dangulbi da kuma Gusau zuwa Magami.

Da yake nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ‘yan bindiga suka sake kunno kai da kuma kashe-kashen da aka yi wa wasu mutanen da ba su jiba ba su gani ba a baya bayan nan a kananan hukumomin Gusau, tsafe, Gummi, Bukkuyum, Anka, Bungudu, Maru, Maradun da Kauran Namoda, gwamnan ya kuma shawarci duk masu ruwa da tsaki da aka gayyata taron jami’iyar APC na yau Jumma’a, da su dakata har sai an fitar da sabuwar rana.

Gwamnati jihar ta umarci jami’an tsaro da su dauki mataki kan duk wadanda aka samu da saba wannan umarni.

Labarai Makamanta

Leave a Reply