Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnan Jihar ya lula ?asar waje, lokaci ka?an bayan kwashe ?aliban Islamiyya da ‘yan bindiga su ka yi, a Tegina, cikin ?aramar Hukumar Rafi.
Sai dai kuma Kakakin Ya?a Labarai ta Gwamnan, Mary Noel-Berge ta ce ya tafi laluben hanyoyin da zai ?arfafa tsaron jihar ne. Sannan kuma ta ce ya tafi ne tun kafin a sace yaran.
Ta ce Gwamnan ya tabbatar wa iyayen yara cewa ana nan ana ?o?arin ganin an ?wato ko an ceto yaran na Tanko Saliu Islamiyya da aka sace a garin Tegina, bayan ‘yan bindiga sun mamaye garin kuma sun ?wace ofishin ‘yan sandan garin na Tegina.
Gwamna Abubakar Bello ya ce ya umarci jami’an tsaro su tabbatar cewa sun ceto yaran cikin ?an?anen lokaci.
Sanarwar ta ce ya fita ne domin laluben yadda za a inganta tsaro a jihar Neja, wadda ‘yan bindiga da Boko Haram su ka samu gindin zama a ciki, kamar yadda Gwmnan da kan sa ya taba furtawa.
Mary ta ce ba da?ewa Gwamna Abubakar Bello zai yi ba, da ya kammala sha’anin da ya kai shi, zai koma gida Jihar Neja.
Wannan ne karo na biyu da aka sace ‘yan makaranta a ?aramar Hukumar Rafi, a cikin 2021. Domin a can ne aka sace ?aliban sakandare na Kagara, a farkon wannan shekara.