Matsalar Tsaro: Gumi Ya Yi Ganawar Sirri Da Obasanjo

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban ?asa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa shahararren malamin na can a yanzu haka suna gudanar da taro da Obasanjo a gidan tsohon Shugaban kasar.

An ruwaito cewa malamin ya isa gidan tsohon shugaban ?asar dake garin Abeokuta da misalin ?arfe 11:00 na safiyar yau Lahadi. Mai taimaka ma Obasanjo kan harkokin ya?a labari, Kehinde Akinyemi, ya tabbatar da zuwan malamin ga manema labarai ya kuma ce akwai wasu shugabannin addinai da suka halarci taron.

“Eh hakane, yanzun haka Gumi na tare da Baba (Obasanjo) suna tattaunawa tare da wasu shugabannin addinai,” inji Akinyemi da aka tambayeshi kam zuwan malamin.

Kwanan nan, malamin ya tattauna da tawagar yan bindiga daban-daban a jihohin Zamfara da kuma Neja don ganin sun saki mutanen da suka kama.

Dr. Gumi ya kuma kira yi gwamnatoci da su baiwa yan bindiga dama don su shiryu. A cewar malamin, sakamakon tattaunawar da yake yi da yan bindiga yana fidda ?a mai ido, duk da cewa ana cikin damuwa da ayyukansu.

Ya ce kowacce tawaga tana gaya mana ?orafin su wanda abu ne mai sau?i. A mahangar malamin za’a iya warware wa?annan matsalolin nasu cikin sau?i.

Related posts

Leave a Comment