Matsalar Tsaro: Dr. Gumi Na Cigaba Da Ganawa Da Fulani

Cikin alkawarin da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi lokacin da ya tattauna da fulanin dajin Jere a ranar 3/1/2021 domin kawo karshen rashin zaman lafiya da kidnapping da kashe-kashe a hanyar Abuja. Na samar musu da makaranta da Asibiti da wurin kiwon shanu.

Yau Allah ya azurta Malam da daura harsashin wannan gini kuma yayi masa lakabi da Sheikh Usman bn Fodio Center (Kagarko Grazing Reserve).

In da za a gina musu makaranta da asibiti da wurin da zasu rika shayar da dabbobinsu. Kafin shigarsa dajin sai da ya tsaya fadar Hakimin kagarko domin sada zuminci.

Idan baku manta ba a ranar Lahadi 17/01/2021 Malam ya shiga dajin Rugar Jaja dake Gamagira, Karamar Hukumar Soba dake jihar Kaduna inda suma aka assasa irin wannan cibiya ta Sheikh Usman bn Fodio Center.

Kamar kowane lokaci Malam ya samu rakiyar Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam babban limamin Masallacin Sultan Bello Kaduna tare da Mal Tukur Mamu (Dan Iyan Fika) Babban Editan Jaridar Desert Herald da sauran dalibai da sauran al’umma baki daya.

Wannan itace shigar Malam daji na hudu, inda malam ya dauki alwashin shiga domin tattaunawa tare da kiran jama’ar fulani zuwa ga zaman lafiya da karantar da su da koya musu addinin musulunci.

Allah Ya saka mishi da alkairi tare da dukkan masu taimaka masa a cikin wannan aiki da ya dauko.

Labarai Makamanta

Leave a Reply