Matsalar Tsaro: Buhari Zai Yi Taron Gaggawa Da Shugabannin Tsaro

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gudanar da taro na gaggawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar, a ranar yau Litinin domin sake duba halin da tsaron ƙasar ke ciki.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai Malam Garba shehu ya fitar, ya ce a yayin ganawar shugaban ƙasar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da ƙara ƙaimi a fannonin da ke buƙatar kulawa.

A ‘yan kwanakin nan ne dai Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya a Najeriya suka fitar da jerin gargaɗin cewa akwai barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da Abuja.

Tun bayan bayyanar rahoton jama’a da dama musamman mazauna birnin tarayya Abuja sun shiga damuwa da tashin hankali sakamakon halin fargaba da suka tsinci kansu ciki dalilin rahoton.

Labarai Makamanta

Leave a Reply