Matsalar Tsaro: Buhari Zai Bayyana Gaban Majalisa Ranar Alhamis

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amsa gayyatar da majalisar kasa tai masa a ranar alhamis 10 watan nan da muke ciki.

Ana sa ran shugaban zai gurfana gaban majalisar ne domin amsa tanbaoyoyi musamman kan shakakin tsaron da ya yiwa kasar dabaibayi. Idan ba a manta ba, jaridaar Muryar Yanci ta sha kawo maku ruhoton yadda majalisar dokokin kasar tai ta kiraye kiraye a lokaci da dama da ya sauya shuwagabannin rundunar tsaron kasar.

Ana sa ran tattaunawar shugaba Buhari da yan majalisar zai maida hankali ne kan matsalolin tsaron kasar da tabarbarewar tattalin arziki da Najeriya ke fama dashia halin yanzu.

Ko a jiya lahadi, Muryar Yanci ta kawo maku tuhoton yadda wasu manbobin majalisar kasar nan karkashin babban jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci yayanta na majalisar da suyi gaggawan tsige shugaba Buhari musamman kan gaza kawo wa kasar tsaron da yai rantsuwa zai yi lokacin rantsar dashi. Sannan

Wace irin tambaya kuke so yan majalisun ku su yiwa shugaba Buhari idan ya gurfana gaban su ranar alhamis?

Related posts

Leave a Comment