Matsalar Tsaro: An Soki Lamirin Buhari Akan Nuna Halin Ko In Kula

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC kuma masoyin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya caccaki shugaban kasar kan matsalolin dake faruwa amma bai yi magana ba.

A jiyane dai Adamu ya caccaki shugaban kasar kan zanga-zangar SARS inda aka kama wanda suka fita zanga-zangar. Yace suna da ikon yin zanga-zanga.

A yau kuma Adamu ya caccaki shugaban kasar ne kan matsalar kashe-kashe da kuma barazanar fadan kabilanci dake shirin barkewa amma yace shugaban kasar yayi shiru bai ce komai ba da zai kwantar da hankulan mutane.

Yace shin wai me yasa duk irin wannan abu idan ya faru, sai ‘yan Najeriya sun yi ta Magana da Roko, sannan ne shugaban kasar zai dauki mataki? Yacs ya kanata dai shugaban kasar yasan abin yi kamin lamari ya kazance.

Related posts

Leave a Comment