Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya bukaci gwamnatin tarayya ta bari mutane su mallaki bindigogin kansu domin kare kansu da iyalansu saboda yadda matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.
Gwamna Ishaku ya bayyana haka ne ranar Talata yayinda shugabannin kananan hukumomin jihar suka ziyarceshi bayan jana’izar daya daga cikinsu da ‘yan bindiga suka kashe.
Gwamnan ya yi alhinin tsanantan rashin tsaro, inda Najeriya bata taba shiga irin wannan halin ba. “Matsalar tsaro a kasar nan tayi munin da bata taba yi ba kuma ya zama wajibi mu tashi tsaye.
Mu a matsayin shugabanni mun bada shawawarin mu domin kawo sauyi, ba zai yiwu ku cigaba da abu daya kuma ku saurari wani sakamako daban ba,”.
“Idan mun gaza baiwa al’ummarmu tsaro, mu bari su mallaki AK-47, saboda idan kowa na da lasisin AK-47, na rantse babu wanda zai zo gidanka.”
Gwamna Ishaki ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu musamman iyalan shugaban karamar hukumar Ardo-Kola, Salihu Dovo, da aka kashe.