Gamayyar ƙungiyoyin Arewa CNG tace zata fara zanga-zanga tutur daga ranar yau Alhamis akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Najeriya, har sai abin da hali ya yi.
Kamar yadda kungiyar tace, za ta yi hakan ne don sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin halin da jihohin arewa 19 suke ciki.
Kungiyoyin na Arewa sun ce, gwamnonin arewa sun gaza akan bai wa rayuka da dukiyoyin ‘yan arewa cikakken tsaro, don haka tura ta kai bango. Ba a harkar tsaro kadai gwamnonin suka kasa ba, har da karin kudi akan asalin kudin wutar lantarki.
“Mun fahimci cewa shugaban kasa da gwamnoni basa yin wani kokari wurin daidaitawa da malaman jami’a. CNG ta kula da yadda harkar tsaro ta lalace a arewa, kuma gwamnati bata yin komai akai.
Sun kara da cewa, shugaban kasa ya kalmashe hannu ya zura wa dubbannin ‘yan Najeriya ido, ‘yan bindiga suna ta wahalar dasu. Tura ta kai Bango ya isa haka!