Matsalar Najeriya: Babu Ruwan Allah – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi aiki tukuru tare da yin addu’a domin samun nasarar kasar nan a sabuwar shekara mai kamawa, kamar yadda today.ng ta rawaito.


Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.


Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Obasanjo ya nuna ?in amincewarsa cewa, Allah ne ya ?addara halin talauci da Najeriya ke ciki, inda ya dora alhakin hakan ga shugabannin da suka jefa ta cikin wannan mayuwacin halin.

A cewarsa, “Bai kamata mu rinka dorawa Allah laifin halin da ?asar mu ke ciki ba, dole mu zargi kanmu, Najeriya bai kamata ta zama talaka ba, bai kamata ?an Najeriya ya kwanta da yunwa ba”

“Halin da muke ciki za?i ne na shugabanni da mabiya. Addu’ata shine Ubangiji Ya sa shekarar 2021 ta zame mana alheri ga kowa, amma haka ba zai faru ba sai mun ha?a da aiki tukuru”

Ya sake jaddada bukatarsa ga yan Najeriya cewa matu?ar suna son tabbatar Najeriyar da suke so, wajibi ne su tashi aiki tukuru sannan su ha?a da addu’a, don tunkarar kalubalen dake gaba.

Related posts

Leave a Comment