Tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari ya shaida wa gwamna Bello Matawalle cewa zai rasa kujerarsa muddin ya bar jam’iyyar PDP, bisa shari’ar kotun koli da ta bashi nasarar samun mulkin a 2019.
Yari ya shaida hakan ne a ofishin jam’iyyar APC da ke birnin Gusau a jiya Lahadi lokacin rabon kayan abincin ramadan ga magoya bayan APC a cewar Jaridar Punch ta Najeriya.
Tsohon gwamnan wanda Sanata Kabiru Marafa ya wakilta na cewa babu wani mutum da ya sanar da su ta baka ko a rubuce cewa Matawalle ya koma APC.
Ya kuma yi garga?in cewa tunda kotun koli ta soke nasarar APC da sanar da PDP a matsayin wacce ta yi nasara kuma dole ta ci gaba da mulki har 2023.