Ma’aikatar Harkokin Agaji da Jinƙai ta bayyana cewa jimillar matasa 5,042,001 ne su ka yi rajistar shiga kashi na uku (Batch C) na shirin tallafi na N-Power.
An rufe rajistar shiga shirin ne a ranar Lahadi da ta gabata, wato 9 ga Agusta, 2020.
Rajistar, wadda aka fara ta a ranar 26 ga Yuni, 2020, an so kammala ta ne a ranar 26 ga Yuli amma sai ma’aikatar ta ƙara mako biyu don a bai wa waɗanda ba su yi rajistar ba damar shiga.
Ministar Harkojin Agaji da Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa za a bi dukkan matakan da su ka kamata don tabbatar da cewa sai wanda ya cancanta ne za a zaɓa domin cin moriyar shirin.
A cikin sanarwar da mai taimaka wa ministar kan harkar yaɗa labarai, Halima Oyekade, ta raba wa manema labarai a ranar Litinin, an bayyana cewa ma’aikatar za ta tabbatar da cewa za a riƙa sanar da waɗanda su ka yi rajistar da ma sauran jama’a dukkan halin da ake ciki game da shirin.
Hajiya Sadiya ta ƙara da cewa manufar shirin na N-Power shi ne a ba wa matasa damar samun horo na samun aiki ko sana’a wanda hakan zai taimaka sosai wajen gina tattalin arzikin ƙasar nan bayan annobar korona, wato Covid-19.
A cewar ta, za a ba mata da naƙasassu fifiko a wajen zaɓar waɗanda su ka yi rajistar.
Sadiya Umar Farouq ta ce ma’aikatar ta ta sadaukar da kan ta wajen ganin an cimma burin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara a cikin shekara 10, kuma ta lura da cewa shirin N-power na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen cimma wannan ƙudirin.