Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Asiwaju Bola Tinubu, dan yakarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, ya gabatar da sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023 ga Hukumar INEC.
Tinubu ya gabatar da sunan nasa ne lokacin cikar wa’adin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta dibar wa jam’iyyun siyasa don su gabatar da sunayen yan takararsu na zaben 2023.
A halin da ake ciki, jam’iyyar ta tsinci kanta cikin cece-kuce yayin da kungiyoyi a cikin jam’iyyar suka mayar da tsarin zabar abokin takara ya koma kamar gasar addini da kabilanci.