Mata Sun Samu Kyakkyawan Cigaba A Mulkin Buhari – Ministar Mata

An bayyana cewa Mata sun samu kyakkyawan cigaba a ƙarƙashin shugabancin Shugaban kasa Buhari ta fuskoki da dama, kuma hakan wani abu ne na a yaba da nuna godiya akai.

Ministar kula da harkokin Mata Madam Pauline Tallen ce ta bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a cikin shirin “Baƙonmu Na Mako” da gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya saba gabatarwa.

Ministar ta bayyana cewa Mata a karkashin mulkin Buhari sun samu wakilci, kuma Shugaban ya bada dama sosai domin sauraren koke koken su, da shiga cikin al’amurran su, fiye da sauran gwamnatocin baya.

Pauline Tallen ta bayyana cewar Mata sune suke da kashi 60 cikin 100 na adadin jama’ar Najeriya, kuma shakka babu duk wanda ka gani a duniya Mace ce ta haife shi, lallai Mata ba waɗanda ya kamata ace ana watsi da sha’anin su ba ne.

“Duk inda aka wayi gari ya zamana mafi yawan jama’a ba’a harkokin kasa da su to babu shakka wannan ƙasa ta samu naƙasu”.
Mata suke da yawa sune masu zaɓe idan babu su a cikin harkokin ƙasa akwai matsala.

Dangane da batun aikata fyade da ya zama ruwan dare a wannan lokaci kuwa, Ministar ta bayyana kwararan matakai da ma’aikatar ta ke ɗauka akai, inda ta yi kira ga iyaye da su tashi tsaye wajen sanya idanu akan mu’amalolin ‘ya’yan su, da sanar da hukuma duk wani da ba’a yarda da take taken sa ba.

Ministar ta kuma buƙaci malaman addini da su cigaba da yin kira da wayar da kan mabiyan su akan abin da Allah yace dangane da hakkin Mata, domin babu wata jama’a da zata cigaba muddin ana cutar da Mata a cikin ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply