Shahararren dan kwallon kafar Brazil wanda ake ganin ba’a taba samun irin sa a kwallon kafa a duniya ba Pele ya koma ga mahaliccin sa a yammacin ranar alhamis ya na da shekaru 82 a duniya.
Tsohon dan wasan dai ya dauki lokaci yana jinyar cutar kansa da bugun zuciya da kuma koda.
Ko a farkon wannan makon sai da ya fitar da wani faifan bidiyo da yake bankwana da ‘yan uwa da abokan arziki, lamarin da ya sanya daya daga cikin ‘ya’yan sa mata ke cewa zata ci gaba da zama wajen jinyar sa.
A zamanin da yake taka leka, tsohon zakarar gasar lashe kofin duniya karo uku, ya zura kwallaye dubu daya da 281 a cikin wasannin dubu daya da 363 a tsawon shekaru 21 da ya yi yana wasa.
Pele dai shine kadai dan wasan kwallon kafa da ya taba lashe gasar lashe kofin duniya sau uku a shekarar 1958 da 1962 da kuma 1970.
A shekarar 2000 ne dai hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana Pele a matsin gwarzon dan wasan kwallon kafa na karni.
Babu wani dan wasa da ya yi fice wajen daukaka sunan kwallon kafa kamar Pele.