Gwamna Bello Masari na Jihar Katsina ya nuna matu?ar damuwa dangane da yadda masu shari’a da kotuna ke sakin ‘yan bindiga, masu fya?e da sauran masu aikata muggan laifuka da sunan beli.
Masari ya nuna wannan damuwar jim ka?an bayan ya rantsar da sabbin al?alan manyan kotuna guda uku na Jihar Katsina.
Daga nan sai ya yi kira ga ?ungiyar Lauyoyi ta Najeriya cewa ta ja kunnen mambobin ta, su daina fakewa da ‘yancin ?an Adam su na ?aure wa muggan masu laifi gindi ana sakin su.
“Mu na cikin yanayi na babbar matsalar tsaro cike da barazana. Don haka tilas sai mun ha?a kai wuri ?aya, domin magance wa?annan ?alubale.”
“Mun sha samun rahoto ko ganin yadda aka bada belin ‘yan bindiga, ‘yan fashi da makami da masu aikata fya?e, amma daga baya kuma su sake aikata laifin da su ka yi aka kar?i belin su.
“Irin wannan mummunar ta’asa ai da ba a bada belin su ba, ba za su sake samu damar maimaita irin ta ba.” Inji Masari.
Ya kuma yi kiran da a ri?a gaggauta yanke hukunci ana yi wa mai gaskiya adalci.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ?angarorin shari’a ke nuna juna da yatsa, su na ?ora wa juna laifin matsalolin da ke dabaibaye shari’u.
Ya kuma umarci kwamitin da ya kafa cewa su binciki mummunar halayyar yadda ake yawan sakin masu aikata fashi, ‘yan bindiga da masu aikata fya?e da sunan wai an bada belin su.
Daga nan ya ce sabbin Manyan Al?alan Babbar Kotu ?in da ya na?a su ?auki aikin da aka ?ora masu a matsayin damar jajircewa su yi aiki tu?uru, tare da nuna kishi.