Masarautar Zazzau: An Shiga Zagaye Na Biyu Wajen Fidda ‘Yan Takara

Yunƙurin farko na naɗa sabon Sarkin Zazzau ya ci tura inda a yanzu haka masu zaɓe na Masarautar Zazzau suke sake nazari kan sabon matakin zaɓen Sarki.

A ranar Laraba da yamma ne gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Malam Nasir el-Rufa’i ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa, ”A yanzu haka masu zaɓen sarki na sake sabon nazari don zaɓo waɗanda za a zaɓa cikinsu da zai zama Sarkin Masarautar Fulani ta Zazzau na 19.

”Gwamnatin jihar Kaduna ce ta bayar da umarnin yin sabon zagaye na zaɓen bayan da ta soke na farko da aka fara, inda aka cire ƴan takara biyu.

A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa soke zaɓen farkon na da alaƙa da cire sunayen wasu ‘yan takara biyu waɗanda suka nuna sha’awar sarautar amma daga baya aka ce musu an rufe karbar sunayen masu son zama sarki.

Gwamnatin jihar ta kuma nuna ɓacin ranta dangane da yadda aka tsegunta batun zaɓen da masu zaben sarki suka yi a ranar 24 ga watan Satumba tun kafin gwamnan jihar ya samu rahoto a hukumance kan zaɓen.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba ne Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Tun bayan rasuwar sarkin, gwamnan jihar ya tsiri karatun litattafai daban-daban inda a halin yanzu ya karanta aƙalla litattafai uku kamar yadda ya bayyana.

Ya ce littafan za su taimaka masa wurin yanke hukunci a zaɓen sarkin ganin cewa shi ne mai wuƙa mai nama a ƙarshen zaɓen.

Labarai Makamanta

Leave a Reply