Manufofin Tinubu Suna Da Kyau Sai Dai Ya Gamu Da Kurakurai – Obasanjo

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya soki yadda ake aiwatar da manufofin shugaba Tinubu, duk da cewa ya amince da muhimmancin su. Maganarsa tasa ya zo daidai da bukukuwan cikar Tinubu shekara guda kan karagar mulki.

Obasanjo ya yi tsokaci ne na musamman kan wasu hukunce-hukuncen gudanarwa guda uku da suka hada da cire tallafin man fetur, yadda ake tafiyar da farashin canji, da Kuma martanin da sojoji suka dauka a Jamhuriyar Nijar.

A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, wanda ya bayar da sanarwa a Abeokuta a ranar Lahadi, Obasanjo ya yi magana a wurin taron Paul Aje Colloquium (PAC) da ke Abuja kan taken “Ci gaban Najeriya: Kewaya Hanyar fita daga cikin Tabarbarewar Tattalin Arziki da rashin tsaro a halin yanzu.”

Obasanjo ya soki Gwamnatin Tinubu, yana mai cewa, “Gwamnatin da ke yanzu ba ta sami hanyar da ta dace ta tafiyar da tattalin arzikin kasar ba don samar da kwarin guiwa da amana ga masu saka hannun jari su fara.

Ya kara da cewa, “Gwamnati ta dauki muhimman matakai guda uku. Biyu daga cikinsu – cire tallafin da kuma rufe gibin da ke tsakanin kasuwar ba?ar fata da farashin canji na hukuma – ya zama dole amma ba a aiwatar da shi ba da kyau ba, wanda ya haifar da talaucin tattalin arziki da ‘yan Najeriya. Batu na uku shi ne yadda ake tafiyar da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.”

Related posts

Leave a Comment