Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe a kauyen Kashobe da ke Jihar Borno ya kai akalla 110, sabanin 70 da Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar bayan ya halarci jana’izar 43 da aka tattara gawarwakinsu yau da safe.
Shugaban Aikin Jin-kai na Majalisar Edward Kallon ya bayar da wannan sabon adadin wanda ya ritsa da fararen hular da ke aiki a gonar shinkafa.
Zulum da ya jagoranci jana’izar mutanen 43 ya ce, adadin na iya kai wa 70 saboda batar wasu mutane wadanda ba a iya gano inda suke ba.
Wannan shi ne karo na biyu da mayakan Boko Haram ke hallaka manoman a cikin wata guda, bayan 22 da suka kashe a watan jiya, lokacin da suke aiki a gona.
Harkar tsaro dai a yankin Arewacin Najeriya na ƙara shiga cikin wani mawuyacin hali, lamarin da masu fashin baƙin al’amurra ke ganin yankin ya shiga taskun da a baya can bai shiga ba.
Shugaban ƙasa Buhari dai na cigaba da fuskantar suka da matsin lamba daga kungiyoyin daban daban bisa halin da Arewacin Najeriya ya shiga ciki, inda ake ganin ya gaza gaba ɗaya.