Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba su ka yi batan dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga Babban Bankin Najeriya CBN a Shekarar da ta gabata.
Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafan Najeriya, shiya jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan inda yace Manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noman rani, sannan aka neme su daga baya domin biyan bashin aka rasa.
A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan. Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace kudin da manoman kungiyarsa suka karba bashi sun ki biya, kuma da dama cikinsu sun gudu.
Andami ya bayyana mamakin dalilin da zai sa manoma su ki cika alkawuran da suka dauka ba. Yace: “Babu ko daya cikinsu yanzu haka da ya dawo da kudin bashin da aka bashi, kuma da dama cikinsu sun gudu.”
Babban Bankin Najeriya CBN ya basu bashin ne domin inganta noman shinkafa cikin manufar gwamnatin tarayya na ciyar da kasa da shinkafa ba tare da an shigo da su daga kasar waje ba.
An ba Manoma daga kananan hukumomin Lau, Gassol, Wukari, Karim-Lamido, Ardo-Kila da Jalingo karkashin kungiyoyin hadin kai 185. A cewar mataimakin shugaban kungiyar, Daniel Gani, ya ce yawancin manoman sun yi tunanin kyauta gwamnatin Buhari ta basu.
Ya kara da cewa wasu daga cikin manoman sun canza lambobin wayoyinsu da adireshin da suka bada, har yanzu ba’a samu nasarar samunsu ba. Ya ce duk da cewa kungiyar na farfadowa ne yanzu, za ta iyakan kokarinta wajen ganin an kwato kudin bashin daga hannunsu.