Mali: Sojoji Sun Yi Alkawarin Gudanar Da Sahihin Zaɓe

Sojojin da suka hamɓarar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta sun bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.

Wannan ya biyo bayan bayyanar shugaban a kafar talabijin, inda ya ce ya sauka daga muƙaminsa.

Sojojin sun yi awon gaba da shi tare da firaministansa daga babban birnin ƙasar zuwa wani sansanin soja.

Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta AU da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

Shugabannin rundunar sojojin Mali sun bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasar tare da sanya dokar hana fita da dare, a cewar wata sanarwa da mataimakin shugaban ma’aikatan sojojin sama na ƙasar.

“Daga yau, 19 ga watan Agustan 2020, an rufe dukkanin iyakoki na sama da na ƙasa har sai baba ta gani. An saka dokar hana fita daga ƙarfe 9:00 na dare zuwa 5:00 na asuba har sai baba ta gani,” in ji Kanar-Manjo Ismaël Wagué a wani jawabin talabijin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply