Malaman Jami’o’i Zasu Koma Bakin Aiki A Shekarar Baɗi – Gwamnatin Tarayya

Bayan kwashe kusan shekara daya da kungiyar malaman jam’i’o’i suka yi a gida suna yajin aiki wanda ya tilasta dalibai zaman dirshan na kimanin shekara guda, Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran malaman za su koma aji a watan Janairun 2021.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba. Ya tabbatar da cewa sun kai wani mizanin daidaitawa da kungiyar malaman jami’o’in da ya kai kashi 98 cikin 100.

Ministan ya tabbatar da cewa ragowar kashi biyun ba wani abun dubawa ne, lamurra ne da za a iya hakuri da su.
“Mun cika burikan ASUU kusan kashi 98. Dan ragowar abubuwan da ba a rasa bane. “A don haka nake fatan cikin daren yau mu kammala sauran ayyukan da ya dace mu yi.

Su ma suna da wasu kananun ayyukan da ya dace su yi da jama’arsu. “A ranar Talata muke sa rana za mu hadu da rana sannan mu sake tattaunawa. Akwai yuwuwar mu kawo karshen yajin aiki idan muka hadu a yau.”

A wani labari na daban, taron da gwamnatin tarayya da ASUU suka yi a ranar Alhamis wanda kowa yayi fatan za a cimma gaci ya kare ba tare da wata nasara ba.

Ya kamata a fara taron sirrin da misalin 4pm a dakin taron ma’aikatar kwadago da ayyuka, amma sai 5:20pm aka fara, sannan aka gama 8:18pm, sannan wadanda suka halarci taron sun ki sanar da manema labarai abinda suka tattauna.

Kafin a fara taron, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce rashin halartar taron da wuri yana da nasaba da rashin karasa tuntubar ma’aikatar kudi sai a safiyar Alhamis.

Labarai Makamanta

Leave a Reply