Makon Shayarwa: An Shawarci Magidanta Su Rika Tsotson Nonuwan Matansu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kodinetan Cibiyar Kiwon Lafiya a matakin farko da ke Uyo, Peace Essien, ta yi kira da a rika jawo hankalin Iyalai da al’umma da kuma malaman addini sanin mahimmancin shayar da nonon uwa ga jarirai.

A cewar jami’a Essien, mahaifin yaro wato baban sa na da muhimmiyar rawa da zai taka kafin mai dakin sa ta haihu wajen ganin kafofin nonuwa sun bude sannan su kasance a shirye don ciyar da jariri.

Essien, yayin da yake zantawa da manema labarai a Uyo kan makon shayar da jarirai ta duniya na 2023, ta ce goyon bayan al’umma da iyali na da matukar muhimmanci wajen samun nasara a harkar shayar da jarirai nonon uwa zalla.

Ta ce ya kamata a ce an fara shayar da jariri nonon uwa minti 30 bayan an haifi da, sannan a ci gaba da haka har sai ya kai watanni shida cur yana kwankwadar nonon.

” Ya kamata a shi ma maigida, ya yi na shi aikin, ba kawai dawainiyar mai dakin sa ba dole sai ya taimaka wajen inganta nonon domin jaririn ya ji dadin sha.

” Maigida zai rika tsotsar nonon matar sa akai akai, domin ya bude kafofin da ruwan nonon zai rika fita idan jariri ya zo duniya. Idan ba zai iya tsotsa ba, ya rika shafa shi yana mulmula nonon.

A karshe ta yi kira ga iayaye da mata masu ciki da su rika zuwa awo akai akai a lokacin da suke da juna biyu sannan a dage da shayar da jariri, nonon uwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply