Hajiya Halima Iliya, shugabar shirin samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasa, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.
A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ƙasar.
Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja. A cewar hukumar.
A ranar Alhamis da ya wuce ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.
Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ƴanbindigar suka sace ɗaliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.
Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ƴangudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ƴanBoko Haram da aikatawa.
Iyaye da ƴan’uwan ɗalibai da sauran waɗanda aka sacen na ci-gaba da roƙon gwamnati ta kuɓutar da su.