Makamai Jami’an Tsaro Ke Bu?ata Ba Addu’a Ba – El Rufa’i

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya ce hukumomin tsaron Nijeriya suna bukatar makamai na zamani ba addu’a ba kafin su iya magance ta’addanci da ‘yan ta’adda dake addabar kasar musamman yankin Arewacin Kasar.

El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayin taro na musamman da aka gudanar tsakanin gwamnonin jihohin arewa maso yamma da Malaman addinai gami da sarakunan gargajiya a Kaduna Cibiyar Arewa.

Mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ne ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya a wurin taron wanda aka shirya domin lalabo hanyar kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso yammacin ?asar.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da batun tsaro ya shafi kowa, ya kamata gwamnati ta bashi kulawa ta musamman, fiye da komai domin duk kasar da ta wayi gari ba ta da tsaro to tabbas tana cikin ru?ani.

“Akwai masu ruwa da tsaki da dama da basu samu damar halartar wannan taron ba saboda an aika musu gayyata a cikin takaitaccen lokaci.

“Kullum ‘yan bindiga kara samun karfin gwuiwa suke yi, har sojoji suke kai wa hari. Wasu gani ma suke yi tamkar babu wani abu da ake yi akan matsalar tsaro.

“Akwai bukatar mu ba hukumomin tsaro gudunmawa, amma ta makaman zamani ba ta addu’a ba. Alhakin tabbatar da tsaro ya rataya akan wuyan kowa,” a cewar El-Rufa’i.

Indai jama’a basu manta ba mun ruwaito cewa wata tawaga a karkashin mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Babagana Monguno, za ta fara gudanar da wani rangadi domin neman mafita akan matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasa.

A cikin wata sanarwa da Monguno ya fitar ranar Lahadi, ya ce tawagarsa za ta fara ganawa da gwamnonin jihohin arewa maso yamma a garin Kaduna ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu.

A cewarsa, an kirkiro wannan tsari ne na ganawa da shugabannin da masu ruwa da tsaki domin samar da tsaro da zaman lafiya mai dorewa a kasa.

Related posts

Leave a Comment