Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kudurin Nema Wa Talaka Sauki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar wakilai ta ƙi amincewa da ƙudirin neman ta dakatar da ƙarin farashin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan Majalisar ta ƙi amincewa da ƙudirin ne saboda a cewarta ta kafa kwamiti wanda zai yi bincike kan dalilin yin ƙarin.

Ƴan majalisar wakilan dai sun yi watsi da kirayen-kirayen na dakatar da ƙara farashin kuɗin man fetur daga N537 zuwa N617 kan kowace lita ɗaya, wannan dai na zuwa ne kusan kwana shida bayan ƴan majalisun sun amince a basu tallafin N70bn daga cikin tallafin N500bn da aka shirya domin rage raɗaɗin cire tallafin farashin man fetur.

A zaman majalisar na ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, majalisar ta yi watsi da ƙudirin dakatar da ƙarin farashin man fetur da komawa kan tsohon farashi na N537 kan kowace lita, maimakon hakan, majalisar ta amince da kafa kwamitin da zai binciki dalilin ƙarin kuɗin man fetur da na kuɗin ababen hawa ba zato ba tsammani a faɗin ƙasar nan.

Majalisar ta kuma buƙaci kwamitin da ya samo hanyoyin bayar da tallafi da za a bi domin tsamo ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da su ke ciki. Majalisar wakilan ta bayyana cewa tun da har ta riga da ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan ƙarkn kuɗin, dakatar da ƙarin farashin kuɗin man fetur zai zama kamar ƙin barin kwamitin ya gudanar da aikinsa ne.

Sai dai, ƴan majalisar sun amince su kafa wani kwamiti na wucin gadi wanda zai ƙunshi kowane yanki daga cikin yankuna shida da ake da su a ƙasa Read more: https://hausa.legit.ng/news/1544872-yanzu-yanzu-majalisar-wakilai-ta-yi-watsi-da-kudirin-rage-farashin-man-fetur/?fbclid=IwAR37Eo8Rp2L0RIER0PyulMxh9VH_G69cs1u4H

Labarai Makamanta

Leave a Reply